Ma'ajiyar sirri ta manyan shugabannin duniya
October 4, 2021Talla
Rahoton sakamakon binciken da aka fidda, na zama daya daga cikin manyan tonon asiri da aka yi a kan bayanan arzikinsu, wanda ya hada da shugabannin kasashen duniya 35 na da, da na yanzu da sama da tsoffin jami'an gwamnatoci 300, daga kamfanoni da ak sa a takardun Pandora.
Cikin wadanda aka bankado da sirrin hada hadar dukiyarsu da ke boye har da sarki Abdullah na Jordan, da tsohon firaministan Birtaniya Tony Blair da matarsa, da shugaban kasar Rasha Vladmir Putin da Uhuru Kenyata na kasar Kenya da sauransu.
Da dama na amfani da wannan barauniyar hanyar ce ta wawure kudaden al'umma da ma yadda 'yan kasuwa da ke kaucewa biyan kudaden haraji.