An soke tashin jiragen sama 500 a Turai
May 24, 2011Hukumar da ke kula da zirga -zirga jiragen sama a nahiyar Turai ta ce an soke tashi kokuma saukar jiragen sama 500 a yau Talata a faɗin Turai, dalili da gajimarin toka da suka mamaye sararin samaniyar yankin arewacin Turan.
Kamfanin zirga-zirgar jiragen sama na British Aiways ya soke duka tashin jirage tsakanin Landan da Scotland.
A yanzu gajimarin tokar sun turnuƙe wani sashe na sararin samaniyar ƙasashen Island,Nowe da Danmark.Ƙurrarun sun yi hasashen cewar nan zuwa Alhamis al´amarin ka iya shafar sararin samaniyar ƙasashen Faransa da Spain.
Shekara da ta gabata a daidai wannan lokaci wani dutse mai amen wuta shima daga Island a tsawan mako guda ya hana sauka da tashin jiragen sama a wasu ƙasashen Turai, abinda ya haddasa asara mai tarin yawa, da kuma galabaitar fasenjoji.
Mawallafi: Yahouza Sadissou Madobi
Edita: Abdullahi Tanko Bala