Rasha tana binciken harin ta'addanci
October 17, 2018Talla
Kasar Rasha ta bayyana a wannan Laraba cewa za a shiga aikin bincike kan wani abu da ake zargin bam ne da ya tashi a wata makarantar fasaha ta birnin Kerch da ke bangaren yankin Kirimiya da kasar ta Rasha ta yi mamaya daga kasar Ukraine. Fashewar dai ta yi sanadi na rayukan mutane 18 da raunata wasu da dama.
Kwamitin masu bincike da ya nazarci wasu manyan hare-haren ya bayyana cewa ya bude bincike na aikin ta'addanci a kwalejin ta Kerch inda kawo yanzu aka gano wanda ya kitsa harin ya halaka.