SiyasaAfirka
An sanya dokar hana zirga-zirga a Lamurde na jihar Adamawa
July 12, 2025Talla
Gwamnatin jihar Adamawa da ke Arewa maso Gabashin Najeriya ta ayyana dokar ta baci ta hana zirga-zirgar mutane na tsawon sa'o'i 24 a karamar hukumar Lamurde da ke kudancin jihar, bayan samun rahotannin mutuwar kimanin mutane hudu a wani sabon rikici na kabilanci.
Kazalika kwamishin 'yan sandan jihar Dankombo Morris ya kaddamar da kwamitin bincike kan musabbabin afkuwar lamarin, tare kuma da jibge 'yan sandan kwantar da tarzoma a yankin na Lamurde domin tabbatar da doka da oda.
Karin bayani:ISWAP ta dauki alhakin halaka kiristoci a Arewacin Najeriya
Ko a farkon wannan wata na Yuli da muke ci, an samu tashin hankali a kauyukan Lafiya da Boshikiri da ke kananan hukumomin Lamurde da Guyuk a jihar ta Adamawa.