An samu tada jijiyarwuya tsakanin Rasha da ƙungiyar EU.
February 25, 2011Wata taƙaddama ta taso tsakanin Tarayyar Turai da ƙasar Rasha, yayin ganawar Firai ministan Rasha Vladimir Putin da shugaban hukumar Tarayyar Turai Manuel Barroso jiya a Brussel. Batun sauya hanyar shigo da iskar Gas wanda EU ta yi, shine babban abinda ya fi kawo tada jijiyar wuya. Hakan dai yana nufin dole ne kamfanin samar da Gas na Rasha wato Gazprom ya sayar da wasu daga cikin bututun da ya ke turo mai zuwa Turai da su. Putin ya yi gargaɗin cewa sabon shirin zai haddasa ƙaruwar farashin makamashi, kuma masu sayen gas a Turai sune za su ji a jika. EU tace wannan sabuwar dokar shigo da makamashin bawai an yi ta bane don ɓatawa wani, domin har ƙasar Norway ma lamarin zai shafeta, sai dai an ɗauki matakin ne domin hana wani ɓangare yin babakere ta fannin makamashin
Mawallafiya: Pinaɗo Abdu
Edita: Usman Shehu Usman