An samu sabbin shiga a sabuwar gwamnatin Nijar
April 18, 2025Garambawul da shugaba Tianiya yi wa majalisar miistocin gwamnatin tasa ya tanadi kara yawan ministoci daga daga 21 a tsohuwar gwamnatin zuwa 26 daga ciki mata biyar, dukkanninsu a karkashin jagorancin firaminista Mahaman Ali Lamine Zein.Wanda shugaban kasar ya sake bai wa amanar ci gaba da tafiyar da gwamnatin. Ministocin tsohuwar gwamnati 16 musamman sojoji membobin hukumar ceton kasa ta CNSP suka yi nasarar dawowa a cikin gwamnatin da suka hada da ministan tsaro Janar Salifou Modi da kuma na cikin gida birgediya Janar Mohamed Toumba.
A yayin da shugaban kasar ya salami biyar da daga cikin ministocin da suka hada da ministan ayyukan jin kai da rigakafin afkuwar bala'o'i Madame Aissa Lawan Wandarma wacce aka shafe ofishin nata baki daya daga cikin gwamnati, da kuma ministan sadarwa Malam Sidi Mohamed Raliou. Kazalika a sabuwar majalisar ministocin an samu shigowar matasa kamar Sidi Mohamed Ali shugaban kungiyar matasa ta kasa CNJ wanda a yanzu aka nada a matsayin ministan matasa na kasa, da kuma dan fafutika shugaban kungiyar M62 Malam Abdoulaye Seidou.
Wanda ya dare kujerar ministan ksuwanci da masana'antu. Malam Bana Ibrahim shahararren dan fafutikar nan da ya yi fice wajen kare gwamnatin mulkin soja ta CNSP na daga cikin ‘yan gwagwarmayar da ‘yan kasa suka yi hasashen zai shigo sabuwar gwamnatin, amma kuma hakan ba ta tabata ba.