An saki mai caccakar gwamnatin Burkina Faso
July 29, 2025Talla
Hermann Yaméogo mai shekaru 77 a duniya, ya yi batan dabo bayan da wasu mutane dauke da makamai da ba san ko su waye ba suka yi masa dirar mikiya suka yi awon gaba da shi.
Wasu na hannun damansa sun tabbatar wa manema labarai cewa, yana cikin koshin lafiya kuma yana kokarin dawo cikin hayyacinsa. sai dai an kwace wayoyinsa da kwamfutarsa wanda ake zargin cewa za a yi binciken kwakwaf.
Kungiyoyin kare hakkin bil Adama na ciki da wajen Burkina Faso, na Allah wadai da matakan cin zarafi da ake zargin gwamnatin soji na aikatawa kan 'yan adawa, ciki har da kai su fagen daga don yaki da 'yan ta'adda.