An sace wasu faransawa a Nijar
January 8, 2011Wata majiyar tsaro a Nijar ta baiyana cewa wasu mutane da ba a shaida ko su wanene ba sun sace wasu yan ƙasar Faransa guda biyu,a wani gidan abincin da ke a tasakiyar wata babbar unguwa a birnin Yamai babban birnin ƙasar tsakanin daran jiya juma'a zuwa yau Asabar.Shaidu waɗanda su ke yi aikin a cikin wurin sayar da barassar sun ce mutane biyu waɗanda suke lulluɓe da rawani sun ummarci faransawan da su bisu bayan da suka buga tsawa a cikin wurin shakatarwa.
Wannan al 'amari ya auku ne dai a daidai lokacin da gwamnatin ƙasar Faransa ke kokarin yin belin wasu yan ƙasarta guda biyar mai´akatan hakar ma'adanai na kamfanin Areva da na Satom da ƙungiyar Aqmi reshen Alqaida na Magreb ya sace a yankin arewacin ƙasar tun a cikin watan Satumbar da ya gabata.Wakilin DW a Nijar ya ce mutanen da suka yi awan gaba da yan ƙasar ta Faransa guda biyu su na ɗauke da makamai kana kuma suna magana da harshen Faransanci.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Yahouza Sadissou Madobi