Zamfara: An sace sama da mutane 60
August 4, 2025Talla
Mazauna garin Isa Sani sun tabbatar wa da kamfanin dillancin labran Reuters cewa, maharan sun bude wuta kan mutane yayin da suka shiga garin a kan babura da yammacin Asabar biyu ga wannan wata na Agusta da muke ciki.
"Har zuwa yau, ba mu ji wani abu dangane da su ba. Ko'ina shiru,” in ji shi Sufiyanu Ibrahim da ya ce, an sace matarsa kana 'yan bindigar sun harbe shi a kafa.
Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara ba ta yi karin bayani kan sabon harin ba. Wannan na zuwa ne kasa da mako guda, bayan fitowar wani bidiyo da ke nuna mutanen da aka yi garkuwa da su a Zamfara.
Jihar Zamfara mai makwabtaka da Jamhuriyar Nijar, ta zama cibiyar 'yan bindiga da suke kawo cikas ga fannin ilimi da harkokin noma da sufuri da ya tilasta dubban mutane yin hijira.