An kwantar da shugaban Muritaniya a asibitin sojin Faransa
October 14, 2012Talla
Gabannin tafiyarsa Faransa, shugaba Ould Abdel Aziz ya buƙaci 'yan kasar da su kwantar da hankalinsu kasancewar raunin da ya yi bai yi muni ainun ba.
Gwamnatin ƙasar ta bayyana cewa bisa kuskure ne wani soja ya harbi shugaba Ould Abdel aziz lokacin da ya ke dawo daga wani rangadi sai dai kuma wata majiya ta soji ta ce wani mutum da ke kan babur da ba a san ko wane ne ba shi ne ya bude wa shugaban na Murtaniya wuta.
Shi dai shugaba Mohammed Ould Abdel Aziz na daga cikin shugabannin da kekan gaba wajen sanya ƙafar wando guda da masu tsananin kaifin kishin addinin a yankin sahel da ke fama da tada ƙayar baya ta masu gwagwarmaya da makamai.
Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : USman Shehu Usman