An dakile Ebola a gabashin Kwango
September 27, 2022Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango ta bayyana cewa an kawo karshen annobar cutar Ebola da ta barke a gabashin kasar. Ministan kula da lafiya na kasar Jean-Jacques Mbungani Mbanda ya tabbatar da haka cikin wata sanarwa inda ya ce annobar ta kawo karshe a lardin Arewacin Kivu.
Haka ya zama karo na biyar da aka samu barkewar wannan cuta ta Rbola a kasar ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango da ke yankin tsakiyar nahiyar Afirka. Ma'aikatar lafiya ta ce kwanaki 42 aka shafe babu sabon kamuwa da cutar tun bayan da mutum na karshe ya warke.
sai dai a makwabciyar kasar ta Yuganda har yanzu da sauran aiki wajen dakile annobar ta Ebola inda hukumomi suka nuna cewa akwai mutane 18 da ake kyautata zaton sabbin kamuwa da cutar ne.
Tuni mahukuntan kasar ta Yuganda suka tashi tsaye wajen yaki da wannan annoba ta cutar Ebola.