An kashe mutum tara a birnin El-Obeid na Sudan
March 9, 2025Wani hari da mayakan karta kwana na RSF suka kaddamar a ranar Lahadi kan wani birni mai muhimmanci da ke kudancin Sudan ya halaka akalla fararen hula tara tare da raunata 21 a cewar likitoci.
Birnin El-Obeid fadar jihar Kordofan ta Arewa ya kasance fagen daga tsakanin sojojin Sudan da kuma dakarun RSF tun Afrilun 2023.
Kungiyar likitoci ta Doctors Without Borders ta dakatar da aiki a Sudan
Majiyoyi daga babban asibitin birnin sun fada wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa mutanen sun rasu ne sakamakon hare-haren na RSF.
Shaidu sun bada rahoton yadda aka rika ruwan bama-bamai inda wani makami ya fada kan wata motar bas da ke dauke da fasinjoji.
Rikicin Sudan yana daukan hankali
A watan da ya gabata ne sojojin gwamnatin Sudan suka samu damar sa kai cikin birnin bayan 'yan RSF sun shafe kusan shekara biyu suna iko da El-Obeid.