An kashe mutane 20 a wani rikicin kabilanci a gabashin Chadi
June 16, 2025Akalla mutane 20 sun mutu yayin da 16 suka jikkata a wani rikicin kabilanci da ya gudana a wani lardi na gabashin kasar Chadi. A cikin wata sanarwa da suka fitar a birnin N'djamena, 'yan majalisar dokoki 14 na lardin Ouaddaï, sun yi Allah wadai da abin da suke danganta da munanan ayyuka, tare da yin kira ga hukumomin kasar da su kara kokarin tabbatar da tsaron lafiya da dukiyoyin 'yan kasar.
Wata majiya mai tushe ta ce rikicin ya samo asali ne bayan da matasan Zaghawa biyu dauke da makamai suka sace babur na wani dan kabilar Ouaddaï a ranar Talata, lamarin da ya haddasa kazamin rikici. Hasali ma, rikicin ya yi kamari ne a ranar Asabar lokacin da aka kashe akalla 'yan kabular Ouaddaï 12 a wani hari da ‘yan kabilar Zaghawa suka kai.
Karin bayani: Gwamnatin Chadi ta tabbatar da mutuwar mutane 42 sakamakon rikicin kabilanci
Tun dai shekaru da suka wuce ne, gabashin Chadi da ke kan iyaka da Sudan ke fama da rikici tsakanin manoman kakilar Ouaddai da kuma kabilun Larabawa, wadanda makiyaya ne.