SiyasaAfirka
An kashe manoma 14 a Arewa maso gabashin Najeriya
April 28, 2025Talla
Shugaban karamar hukumar Gwoza Abba Shehu Timta ya shaida wa kamfanin dillancin labarai na AFP cewa maharan sun kai farmakin ne a daidai lokacin da manoman ke tsaka da gyaran gonarsu a kauyen Pulka gabanin faduwar daminar bana. Kazalika hukumomi sun ce adadin ka iya karuwa.
Karin bayani: Duniya ta yi watsi da muradun Arewa maso gabashin Najeriya-MDD
Gwamnan jihar Borno Babagana Umara Zulum ya ce janye jami'an tsaro da gwamnatin tarayyar Najeriya ta yi a baya bayan nan ya sake maida hannun agogo baya a kokarin dakile hare-haren 'yan ta'adda da galibinsu ke rayuwa a tsaunukan Mundara da gabar Tafkin Chadi da kuma dajin Sambisa.