Kara kwanakin hutu a Ghana
March 26, 2025A Ghana sabuwar gwamnatin kasar bisa jagorancin Shugaba John Dramani Mahama, ta bai wa al'umman Musulmai a kasar goron Barka da Sallah tun kafin isowar bukuwan na tsawon ranakun hutun bukukuwan daga kwana daya tak zuwa ranaku biyu, abin da ya burge jama'ar kasar.
Karin Bayani: Shirin gwamnatin Ghana na fuskantar matsalolin da kasar ke fama da su
Bayan sanarwar dai a sakon sa na fatan alkheri sarkin zangwannen Ankara baki daya Alhaji Yahaya Hamisu bako, bayan gabatar dashi ya isarda wannan. Sheik Nuh Abubakar Siddik Jihad, da ke jagorantan kungiyoyin jama'a daban-daban 4 da suka hada da IPRC da na addini da ke fatawa kan alqur'ani, ya ce wannan wani takon a yaba ne inda yayi bayani kamar haka.
Manya wadanda suka waye jiya da yau da sanin yadda aka soma har ga isowa wannan gabar, basu boye murnar su ba ga yadda sannu a hankali alkawuran sabuwar gwamnatin NDC ke tabbata. Mai nazarin zamantakewar dan adam Muslim Abdul Rashid, yace shi dai a ganinsa la'akari da wannan damar wanda babu a wani lokacin a baya, wannan wani ci gaba ne na musamman. Amma kuma ga magidanta maza da mata a wannan karon dama ce ta karfafa zumunci.