An kama waɗanda suka saci na'urorin INEC a Najeriya
December 11, 2010Rundunar 'yan sandan Najeriya ta cafke mutane wasu mutane huɗu waɗanda ake zargi da sace sabbin na'urorin ragistar masu kaɗa kuria'a da hukumar zaɓen ƙasar ta INEC ta sayo daga waje. Wani babban jami'in dan sanda yace an yi nasara kama mutanen huɗu ne a birnin Legas kuma za'a gurfanar da su a gaban kotu nan ba da jimawa ba. Ya ƙara da cewa mutanen sun baiwa 'yan sanda muhimman bayanai waɗanda za su taimaka wajen kamo ragowar mutanen da suka hada baki wajen satar na'urorin a filin saukar jiragen sama dake Legas. Hukumar zaɓe ta INEC ta yi odar na'urorin ne domin gudanar da rajistar masu kaɗa ƙuria'a a babban zaben Najeriya da za'a gudanar cikin watan Aprilu na shekara mai zuwa ta 2011.
Mawallafi : Abdullahi Tanko Bala
Edita : Mohammad Nasiru Awal