An kama manyan 'yan adawa a Tanzaniya
April 25, 2025Babban jam'iyyar adawa ta Tanzaniya ta ce an kama wasu manyan jami'anta biyu a kan hanyarsu ta zuwa kotu domin halartar shari'ar da ake yi wa jagoransu da ke fuskantar tuhumar cin amanar kasa. A cikin sanarwar da kakakin jam'iyyar Chadema, Brenda Rupia ta wallafa a shafinta na X da aka fi sani da Twitter a baya, ta ce an kama mataimakin shugaban jam'iyyar da kuma babban sakataren jam'iyyar, wadanda kowa yanzu ba a san inda suke ba.
Karin bayani: 'Yan adawa sun zargi gwamnatin Tanzaniya da kama karya
An dai kama Jagoran adawa na jam'iyyar Chadema, Tundu Lissu, a ranar 9 ga watan Afrilun wannan shekarar bayan gudanar da wani gangamin neman sauya fasalin zabe a kasar. Masu rajin kare hakkin bil Adama a kasar Tanzaniya na zargin gwamnatin Shugaba Samia Suluhu Hassan da amfani da karfin tuwo kan 'yan adawa domin ci gaba da kasancewa kan madafun iko, zargin da gwamnatin Tanzaniya ta musanta.