An kama hanyar kafa gwamnatin hadaka a Jamus
March 9, 2025Akwai alamun nasara a kakorin da jam'iyyun siyasar Jamus ke yi na kafa gwamnatin hadaka, bayan ganawar farko da kawancen jam'iyyun CDU da CSU suka yi da jam'iyyar SPD a kan yadda za a shiga tattaunawa gadan-gadan.
Ana dai sa ran jagoran jam'iyyar CDU, Friedrich Merz zai kasance shugaban gwamnatin Jamus na gaba, bayan nasarar da ya samu a zaben watan jiya.
Friedrich Merz ya ce an ma cimma yarjejeniya kan wasu batutuwa muhimmai dangane da gwamnatin ta hadaka da ake sa rai.
Daga ciki har da abun da ya shafi mayar da baki marasa izinin zama da masu neman mafakar siyasa kasashensu, da kuma batun da ya shafi iyakokin kasa.
Haka nan tattaunawar farkon ya dubi tsarin haraji a Jamus, inda aka tsara rage yawan haraji a kan masu matsakaitan karfi da ke da nauyin gida.
Akwai ma bukatar da jagoran jam'iyyar SPD, Lars Klingbeil ya gabatar a kan dokar zama dan kasa da aka yi wa gyara a baya-bayan da ita ma aka amince da ita, da batun karancin albashi da kuma fansho mai nagarta.