An kaddamar da asusun farfado da tafkin Chadi
January 31, 2025Manufar kaddamar wannan asusu shine bude kofa ga dukkanin kasashe da kungiyoyi da kuma hukumomi da ke son taimakawa domin farfado da tafkin na Chadi.
Tuni kasar Jamus ta bude asusu da zunzurutun kudi Yuro miliyan goma sha daya domin aikin farfado da tafkin sakamkon koma bayan da aka samu sanadiyyar matsalolin tsaro na Boko Haram.
Daraktan kula da magance hadurra da tashe-tashen hankula a ofishin kula da harkokin waje na Kasar Jamus Ms. Anka Feldhusen wacce ta jagorancin kaddamar da wannan asusu ta ce kasar ta na sahun gaba wajen farfado da raya tafkin Chadi tun shekara ta 2019.
Ta ce Jamus za ta ci gaba da hada kai da masu ruwa da tsaki a wannan yankin domin samar dukkanin taimako da tallafi domin raya tafkin Chadi musamman kyautata rayuwar al'umma.
"Ta ce Kalubalen da ke fuskantar tafkin Chadi suna da yawa, matsaloli ne da ke da wuyar sha'ani wadanda suka hada da rashin tsaro da fatara da talauci da matsalolin dumamar yanayi. Ina kira gare ku da ku tallafa wa wannan asusu. Mu a namu bangare za mu ci gaba da tallafawa yankin domin samar da tsaro da zaman lafiya da kyakyawar makoma.”
Kwamred Dauda Muhammad Gombe daya daga cikin masu ruwa da tsaki a harkokin jin kai ne a wannan yankin wadanda ya shaida kaddamar da asusu sun ya ce zai yi tasiri matuka wajen farfadowa tare da raya tafkin.
Wannan dai na zuwa ne a daidai lokacin da aka kammala taron gwamnonin da ke bakin gabar tafkin Chadi wanda aka kwashe kwanaki uku ana gudanarwa a Maiduguri fadar gwamnatin jihar
Gwamnan jihar Yobe Hon Mai Mala Buni shine sabon shugaban kungiyar gwamnonin ya yi karin bayani.
"Akwai maganar habaka kasuwanci, akwai kuma maganar inganta tsaro a tsakanin kashen da kuma maganar gyare gyaren hanyoyin da za su hada wadannan yankunan kamar misali abunda ya hada Kasar Chadi da Kamaru da Nijar da Najeriya.
Al'ummar wannan yankin na cike da fatan za a aiwatar da shawarwarin da aka cimma a wannan taro da yin amfanin da tallafin da aka tara don samar da mafita kan matsalolin da ke addabar yankin.