An ji fashewar boma-bomai a Tehran
June 17, 2025Talla
An ji fashewar wani bam mai karfi cikin wani yanki mai cunkoso a arewacin Tehran babban birnin Iran, yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai hare-hare ta sama.
Ba a dai bayyana ainihin wuraren da aka kai wa harin ba kawo i yanzu, inda ma hukumomi a Iran din suka takaita damar samun intanet, yayin da abinci da sauran kayayyaki ke kara karanci.
Wannan ya biyo bayan hare-haren da Isra'ila ta kai a kan cibiyoyin makamashin nukiliya da cibiyoyin soja a Iran, ciki har da wasu wurare a Tehran din.
Isra'ila ta bayyana cewa hare-haren na nufin dakile shirye-shiryen Iran na samar da makaman nukiliya, tare da kashe manyan jami'an soja da masana nukiliya na Iran.
Sai dai Iran ta ce makamashin nata, ba na yaki ba ne kamar yadda Isra'ilar ke zargi.