An hukunta wasu mata 'yan ƙasashen Turai a Tunisiya
June 13, 2013Talla
Matan Margeurite Stern da Paulmine Stern dukkaninsu 'yan ƙasar Faransa ne a kuma Joshephine Markmann yar' ƙasar Jamus.
Kotun ta same su da laifin yin karan tsaye ga dokoki na al'adu da addini na ƙasar. A cikin watan Mayu da ya gabata ne matan suka yi wata zanga-zanga kusan a tsirara a birnin Tunis, domin matsa ƙaimi ga gwamnatin Ennahda da ta sako wata mata mai suna Amina Tyler wadda ake tsare da ita a gidan kurkuku saboda hotunan da ta bayyana a shafinta na sada zumunta na Fabook a tsirara.
Mawalllafi : Abdourahamane Hassane
Eita : Halima Balaraba Abbas