An harbi wanda ya daba wa malami wuka a Jamus
September 5, 2025Talla
Rahotanni daga birnin Essen a yammacin Jamus na cewa maharin yana samun kulawa a wani asibiti bayan da 'yan sanda suka harbe shi da bindiga a yayin farautarsa.
Bayanai sun tabbatar da cewa malami da aka cakawa wukan yana da shekaru 45, yana kuma koyarwa a wata makarantar koyon sana'a. A baya-bayan nan ana fama da kai hare-hare kan mutane a Jamus.
Babu karin bayani kan halin da malamin ke ciki tun bayan rahotannin farko na cewa yana sashin kula da mara lafiya na gaggawa sakamakon sukar wuka a ciki, jaridar Bild ta Jamus ta ruwaito cewa maharin yana da shekaru 17 kuma dan makaranta ne amma babu karin bayani kan diddiginsa zuwa yanzu.