An harbi ɗan takarar shugaban kasar Kwalambiya
June 8, 2025An harbi dan takarar shugaban kasar Kwalambia da ake ganin shi ne zai iya lashe zaben kasar na badi har sau uku, inda bayanai ke nuna cewa biyu daga cikin harbin ma sun shiga cikin kansa.
Lamarin ya faru ne yayin wani gangamin yaƙin neman zaɓe a Bogota babban birnin kasar.
An kai wa Miguel Uribe Turbay, ɗan shekara 39, hari ne yayin da yake jawabi ga wasu magoya bayansa a wani dandalin shakatawa a jiya Asabar.
‘Yan sanda sun kama wani matashi ɗan shekara 15 da ake zargi da aikata laifin a wurin, a cewar kafofin labarai na yankin.
Uwargidan dan siyasar Miguel Uribe, Maria Claudia Tarazona, ta yi kira ga al'ummar ƙasar da su yi addu’a domin mijin nata.
Ta ce Miguel yana yaƙi ne don tsira da rayuwarsa a yanzu.
Jam’iyyar Centro Democratico ta Uribe ta yi Allah wadai da harin, inda ta ce ya jefa dimukuradiyya da ’yancin faɗar albarkacin baki a Kwalambiya cikin haɗari.