SiyasaAfirka
An kai mummunan harin ta'addanci a Nijar
January 3, 2021Talla
Wasu majiyoyi sun ce mutanen da ‘yan ta’adda suka hallaka za su kai fiye da 100 a cewar kamfanin dillancin labarai na Reuters. Harin ta’addancin na yammacin Asabar din nan ya faru ne a kauyukan Tchombangou da Zaroumdareye da ke kan iyakar Nijar da kasar Mali. An kai harin ne dai a yayin da hukumar zaben Nijar ke kokarin kammala fitar da sakamakon zaben shugaban kasa wanda tuni ta bayyana dan takarar jam’iyya mai mulki Bazoum Mohammed a matsayin wanda ya lashe zagaye na farko. Ana sa ran kuma a gudanar da zagaye na biyu a watan gobe na Fabrairu.