WasanniTurai
An gudanar da jana'izar dan wasan Liverpool Diogo Jota
July 5, 2025Talla
An kai gawar dan wasan na Liverpool Diogo Jota da kaninsa Andre Silva, wata majami'a da ke yankin Gondomar a kusa da birnin Porto na kasar Portugal.
Karin bayani: Labarin Wasanni 20.02.2023
Matar Jota da 'yan uwansa na daga cikin dandazon mutanen da suka halarci jana'izar ciki kuwa har da tawagar 'yan wasan Liverpool da wasu abokan marigayin daga Manchester United da Manchester City har ma da sauran kungiyoyi.
Shugaban kasar Portugal Marcelo Rebelo de Sousa da Firaminista Luis Montenegro sun halarci jana'izar 'dan wasan na Liverpool Diogo Jota.