Ana wasan matasa na Afirka
April 7, 2025
Tafiya ta fara nisa a gasar neman cin kofin kwallon kafa na kasashen Afirka na 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa da ke gudana a kasar Maroko, inda aka shiga wasanni rana ta uku kuma ta karshe a rukunoni daban daban. Amma dai rukunin B ne ya fi daukar hankali, saboda ya kunshi manyan dawa na kwallon wannan nahiya wato Masar da kamaru da ke cikin mawuyacin hali sakamakon rashin tabukan abin kirki a wasanni biyu na farko. Alal hakika ma dai, dan tsakon cikinsu Burkina Faso ta bai wa mara da kanya inda ta samu nasara a duk wasanni uku ciki har da na ranar lahadi inda ta doke Afirka ta Kudu da ci 2-0 kuma ta haye mataki na gaba. Sannan Burkina Faso ta samu tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 'yan kasa da shekaru 17 da za ta gudana a Qatar.
Karin Bayani: Najeriya ta kara wasa mai tasiri
Sai dai a nata bangaren, Kamaru ta fadi ba nauyi a gaban Masar da ci 1-2 a filin wasa na El Bachir da ke Mohammedia, lamarin da ya sa aka yi waje road da ita a gasar kwallon kafar Afirka ta 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa. Wannan dai ya sa Kamaru ta rasa damar buga wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17, inda ta kare a matsayi na karshe a rukuninta na B. Ita kuwa Masar tana da sauran fata na samu tikitin shiga gasar duniya a wasannin tankade da rairaya.
Ita kuwa Afirka ta Kudu ta samu damar hayewa mataki na gana duk da rashin nasara da ta yi, tare da samun tikitin shiga gasar cin kofin duniya na 'yan kasa da shekaru 17 na shekarar 2025.
A rukunin A kuwa, Maroko da ta kasance kungiyar da ta fi zuwa kwallo ya zuwa yanzu ta samu nasara a kan Tanzaniya da ci 3-0, alhahi canjaras kawai take bukata don kai labarai. kuma tuna Lions da l' Atlas ta samu damar hayewa mataki na gaba saboda ta zama ta daya a rukuninta, sannan ta samun tikitin shiga kofin duniya na kwallon kafa na 'yan kasa da shekaru 17 da haihuwa. Ita ma Zambiya da take bukatar canjaras waken kai bantenta, ta yi nasarar lallasa Yuganda da ci 2-1, lamarin da ya kai ta matakin daf da na kusa da na karshe.
A yau, ake kammala wasannin rana ta uku, inda Mali ke karawa da Côte d' Ivoire yayin da Angola ke wasa da Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya a rukunin D. Ita kuwa Senegal ne kece raini ne da Somaliya yayin da Tunisiya ke wasa da Gambiya.
A karshen makon nan ne aka buga wasannin mako na 28 na babban lig kwallon kafar Jamus ba tare da samun sauyi mai ma'ana a teburin Bundesliga ba. Har yanzu dai maki shida ne ke raba Yaya-babba Bayern Munich da ke jan ragama da Bayer Leverkusen mai biya mata baya. Amma dai Bayern ta dandana kudata kafin ta kai ga samun nasara a kan Augsburg da ci 3-1, domin sai da aka ba wa dan wasan Augsburg mai suna Cedric Zesiger jan kati ne Yaya-babba ta fara samun farcen susa. Sai dai, Jamal Musiala dan wasan tsakiya mai kai hare-hare a Bayern Munich ya samu rauni a kafarsa, lamarin da zai iya sa shi rasa wasannin karshen kakar wasanni.
Yayin da ya rage wasanni shida a kammala gasar Bundesliga, Bayern Munich na saman teburi da maki 68, yayin da Bayer Leverkusen da ke rike da kambun zakara ke da maki 62 sakamakon doke Heidenheim da ta yi da ci 1-0. Duk ma da cewar da jibin goshi ne Leverkusen ta samu wannan nasara, amma wannan sakamakon ya faranta ran koci Xabi Alonso:
"A halin yanzu, duk abin da yake da muhimmanci shi ne samun sakamako mai kyau. Idan aka yi la'akari da halin da muke ciki, dole ne mu samu nasara a kowane wasa. An dai shiga wani yanayi a karshen wasan, kuma na yi farin ciki da hakan."
A nata bangaren, duk kuma da cewa Werder Bremen ta gasa mata aya a hannu da ci 2-0, amma Frankfurt ta kasance a matsayi na uku na Bundesliga da maki 48, maki biyu a gaban Mainz, wacce ta yi kunnen doki 1-1 da Kiel. Sai RB Leipzig ta samu ci-gaba bayan nasarar da ta samu a kan Hoffenheim da ci 3-1, lamarin da ya ba ta damar shan gaban Borussia Mönchengladbach, wacce ta tashi 1-1 da FC Sankt-Pauli. Ita kuwa Yaya-karawa Borussia Dortmund ta samu nasara ta biyu a wasanni biyu inda ta yi wa Freiburg cin kaca 4-1, lamarin da ya bai wa BvB damar zuwa matsayi na takwas da maki 41. Duk ma da cewar gurbin gasar zakarun Turai na ci gaba da yi mata nisa, amma kocin Dortmund Niko Kovac ya ce sannu ba ta hana zuwa:
"Mu rika daukar wasa daya bayan daya. Dole ne mu lashe wasannin da suka rage mana, kafin a karshe mu ga inda muka kwana. Nasarar ta yau tana da mahimmanci saboda ta ba mu damar fara wannan makon da kyau, wanda yake da matikar mubimmanci."
Ita dai Borussia Dortmund za ta je kasar Spain domin karawa da FC Barcelona a ranar Laraba a matakin farko na wasan kusa da kusa da na karshe na cin kofin zakarun Turai, kafin daga bisani ta nufi Munich domin buga wasan kare jini biri jini da Bayern a ranar Asabar mai zuwa.
A sauran wasannin Bundesliga kuwa, Stuttgart ta doke Bochum da ci 4-0, yayin da Union Berlin ta samu nasara a kan Wolfsburg da ci 1-0, lamarin da ya sa fita daga rukunin wadanda za su koma karamin lig. A yanzu dai Heidenheim ce ke a matsayi na 16, yayin da Bochum ke a matsayi na 17 da maki 20, ita kuwa Kiel ta zama 'yar baya ga dangi da maki 18.
Yanzu kuma za mu leka sauran manyan lig lig kwallon kafa na kasashen Turai, inda a Faransa, Paris Saint-Germain ta lashe gasar zakarun wannan kasa karo na hudu a jere bayan da ta doke Angers da ci 1-0 a wasan mako na 28 a Ligue 1. Hasali ma, har yanzu kungiyar PSG ba ta barar da ko da wasa guda daya ba tun bayan da aka fara kakar wasanni, lamarin da ya sa ta samun maki 74. Amma kuma Marseille ta koma matsayi na biyu bayan nasarar doke Toulouse da ci 3-2, yayin da Monaco ta sha kashi da ci 2-1 a Brest. Ita kuwa Strasbourg ta dare matsayi na hudu na Ligue din Faransa sakamakon lallasa Reims da ta yi da 1-0. Ita kuwa Lyon da ta samu nasara a kan Lille da ci 2-1, tana a matsayi na biyar.
A Ingila kuwa, Liverpool ta yi rashin nasara a karo na biyu a wannan kakar wasanni, inda ta sha kashi da ci 3-2 a filin wasa na Fulham. Sai dai bai sauya matsayin Reds a teburin Premier League ba, saboda jagorar na da tazarar maki 11 a kan Arsenal a daidai lokacin da ya rage wasanni bakwai a gasar ta Premier. A nata bangaren, Chelsea ta doke Tottenham da ci 1-0, sannan ta koma matsayi na hudu, wato tana gaban Manchester City, wacce ta tashi 0-0 a karawar da ta yi da Manchester United.
A Italiya, Inter Milan na ci gaba da zama jagorar Serie A duk da kunnen doki da ta yi da Parma 2-2. Amma Naples za ta iya kusantarta idan ta yi nasara a karawa da za ta yi Bologna a ranar Litinin da maraice. A sauran wasanni kuwa, Atalanta ta sha kashi a hannun Lazio da ci 1-0 yayin da Juventus ta tashi kunnen doki 1-1 da AS Roma. A halin da ake ciki dai, baya ga tserereniyar lashe kambun zakaran kwallon kafar Italiya, kungiyoyin kasar na gagwarmayar samun gurbi a gasar zakarun Turai. Dalili kuwa shi ne, a daidai lokacin da ya rage wasanni bakwai a gasar Seria A, maki shida ne kawai ke raba Atalanta mai matsayi na uku da Fiorentina mai matsayi na takwas.
A karshe, a kasar Sipaniya ko Spain, Real Madrid ta kasa gane kanta a karawa da ta yi a gidanta da Valencia inda ta sha kashi da ci 2-1 a wasan mako na 30 na La Liga. Yanzu haka dai, Madrid na bayan FC Barcelona da maki hudu, duk da kunnen doki 1-1 da ta yi da Betis. Wannan dai shi ne wasa na 22 da Barca ta yi ba tare da an doka ta ba. A nata bangaren, Atletico Madrid ta murmure bayan nasarar da ta samu a gaban FC Sevilla da ci 2-1.
A wani hali na ba sabon ba, Koriya ta Arewa ta gudanar da gudun fanfalaki na kasa da kasa a titunan birnin Pyongyang a karon farko cikin shekaru shidan da suka gabata, domin murnar zagayowar ranar haifuwar shugaba Kim Il Sung da ya kafa kasar a shekarar 1912. Marathon dai, shi ne gasa ta kasa da kasa daya tilo da ake gudanarwa a Koriya ta Arewa, lamarin da ke ba wa baki damar ganin titunan babban birnin kasar. Rabon Koriya ta Arewa ta shirya gudun fanfalaki tun shekarar 2019, kafin barkewar annobar Covid-19, a lokacin da kasar da ta mallaki makamin nukiliya ta rufe iyakokinta a shawo kan cutar. Amma dai a bana, 'yan tsere na kasashen waje kusan 950 ne suka halarci gasar.
Dan tennis na Amurka Jenson Brooksby, mai matsayi na 507 a duniya, ya lashe kambun ATP na farko a ranar Lahadi bayan da ya doke Frances Tiafoe mai matsayi na 17 da ci 6-4, da 6-2 a gasar ATP 250 na Houston da ke Amurka. Wannan ya ba wa Brooksby mai shekaru 24 damar shiga matsayin 'yan tennis 200 mafi shahara a duniya, inda ya kasance a matsayi na 172. Sannan, gasar Houston ta kasance abin sam barka ga Amurkawa, inda #yan wasansu hudu suka kai matakin wasan daf da na kusa da karshe, lamarin da ke zama farau tun bayan gasar Orlando a 1991.
A Bangaren mata kuwa, Jessica Pegula mai matsayi na 4 a duniya a lokacin fara gasar, ta lashe gasar WTA 500 a Charleston da ke Amurka a ranar Lahadi, inda ta doke wata ba'amurkiyar Sofia Kenin mai matsayi na 44 da ci 6-3, 7-5. Charleston, ya kasance wasan karshe na uku da Pegula ta yi a gasanni hudu, baya ga gasar Miami da Austin. Sannan a yanzu Jessica Pegula ne ke a matsayi na uku a duniya a bayan Aryna Sabalenka ta farko da Iga Swiatek ta biyu a duniya a fagen tennis.