LafiyaArewacin Amurka
Tsohon shugaban Amurka ya kamu da cutar sankara
May 19, 2025Talla
Ofishin tsohon shugban kasar Amurka Joe Biden ya tabbatar da cewa an gano tsohon shugaban yana kamu da cutar sankarar maraina mai saurin yaduwa, kuma yanzu haka likitoci suna duba tsohon shugaban mai shekaru 82 da haihuwa. A makon da ya gabata aka fara ganin alamun cutar ta sankara tare da tsohon shugaban Biden kafin daga bisani aka tabbatar.
Karin Bayani:Zaben Amurka da dangantakarta da Jamus
A watan Janairun wannan shekara ta 2025 Tsohon Shugaba Joe Biden ya ajiye madafun ikon Amurka bayan mulkin tsawon shekaru hudu, kuma a bayan ya kasance mataimakin shugaban kasa lokacin mulkin tsohon Shugaba Barck Obama na tsawon shekaru takwas, kuma Biden ya shafe tsawon shekaru 36 a matsayin dan majalisar dattawa na Amurka daga Delaware.