An gano shirin tsohon shugaban Brazil na tserewa Argentina
August 21, 2025Rundunar 'yan sandan Brazil ta bankado wani shirin tsohon shugaban kasar Jair Bolsonaro na tserewa zuwa Argentina, don neman mafakar siyasa a kasar, a kokarinsa na kaucewa shiga hannun jami'an tsaro.
Rahoton 'yan sandan ya gano cewa ya nemi hakan a cikin watan Fabarairun 2024, a daidai lokacin da mahukuntan kasar ke shirin kwace fasfo dinsa na tafiye-tafiye, ko da yake babu tabbacin ko shugaban Argentina Javier Milei ya amince da wannan bukata a lokacin.
karin bayani:Tsohon shugaban Brazil Bolsonaro ya musanta yin juyin mulki
Mr Bolsonaro na fuskantar tuhumar aikata laifin juyin mulki, ta hanyar yunkurin hambarar da gwamnatin Luiz Inácio Lula da Silva, lokacin da ya so dorewa a kan kujerar shugaban kasar, bayan shan kayi a zaben shekarar 2022.