Najeriya: Kama makamai gabannin zabe
February 23, 2023Matsalar yaduwar haramtattun kanana da manyan makamai tsakanin wadanda da ba su da hurumin rikesu ta jima ta na ciwa hukumomi tuwo a kwarya wanda ake ganin sune ke ruruta wutar rikici da kuma karfafa ayyukan ‘yan ta'adda a Najeriya da kasashe makobta. Wannan ne ya sa cibiyar yaki da yaduwar kanana da manyan makamai ta Najeriya ta mayar da hankali wajen zakulo irin wadannan makamai da ake amfani da su wajen tada hankulan musamman a wannan lokaci da ake shirin yin zabe.
Shugaban wannan cibiya Manjo Janar Abba Dikko ya shaida wa manema labarai a Maiduguri cewa sun kwato dubban makamai kala-kala a hannun ‘yan daba da 'yan ta'adda da zummar samar da yanayi da za a yi zabe ba tare da tashin hankali ba: ''Ba kwato wadannan makamai ba toshe hanyoyin da ake shigo da su shi ne aka fi nuna damuwa me kuke yi na ganin kun dakile shigowarsu'' Sai dai masana tsaro da su ka jinjinawa wannan cibiya bisa wannan nasarar sun ce hakan bai isa ba sai an kara daukar matakai na dakile dukkanin hanyoyi na shigowa da makamai da ma yaduwarsu a cikin kasa da kan iyakokin kasa.