An gano gawarwakin bakin haure a tsibirin Lampedusa
March 19, 2025Rahotanni daga yankin tsibirin Lampedusa na cewa mutane shida sun mutu yayinda wasu 40 suka yi batan dabo, biyo bayan hadarin wani jirgin ruwa makare da 'yan gudun hijira. Hukumomin Italiya na ci gaba da lalubo wadanda suke da sauran numfashi.
Karin bayani: Bakin haure sun cika tsibirin Lampedusa
Shugabar hukumar kula da 'yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya da ke kula da shiyyar Italiya Chiara Cardoletti ta ce akwai yiwuwar mutane da dama sun rasa rayukansu a hadarin jirgin ruwan, kamar yadda ta wallafa a shafinta na X.
Karin bayani: Turai: Damuwa kan kwararar bakin haure
Kamfanin dillancin labarai na ANSA news ya rawaito cewa bakin haure sama da 8,743 suka tsallaka tsibirin na Lampedusa a wannan shekara, kamar yadda ma'aikatar cikin gida ta Italiya ta fitar da alkaluma.