An gabatar da binciken farko na hadarin jirgin Air India
July 12, 2025Binciken kwakkwafin ya gano cewa guda daga cikin matukan jirgin ya sanar da babban kyaftin din jirgin cewa sun samu matsalar na'ura inda ya bukaci dauki ta hanyar amfani da salon "MAYDAY" wajen ankarar da mahukunta halin da jirgin yake ciki a sararin samaniya.
Karin bayani: Mutane 14 sun mutu a hadarin jirgin Indiya
Jirgin na Air India wanda ya yi hadari ne a ranar 12 ga watan Yunin 2025, ya tashi ne daga birnin Ahmedabad da ke yammacin India zuwa birnin Landan na kasar Burtaniya, kafin afkuwar lamarin wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 242 a cikin jirgin da wasu 19 a kasa. Hukumar Kula da Sufurin Jiragen Sama ta MDD ta sanar da cewa za ta fitar da nata rahoton nan da kwanaki 30 masu zuwa, wanda ta gudanar tare da hadin gwiwa da Amurka da Burtaniya.
Karin bayani: Kamfanin jiragen sama na Indiya ya shiga rudani
Mutum guda ne ya tsira da ran sa a hadarin jirgin na Air India, wanda tuni aka sallame shi daga asibiti bayan an duba lafiyarsa.